Kiran da Biden ya yi don sauya tsarin mulki a Rasha
Tun bayan da Joe Biden ya kammala jawabinsa a kasar Poland a daren ranar Asabar da ta gabata inda ya furta daya daga cikin kalamai masu hadari da shugaban Amurka ya taba furtawa a zamanin nukiliyar, kokarin tsaftace bayansa ya yi yawa.